5 Oktoba 2020 - 11:48
Ana Ci Gaba Da Nuna Damuwa Akan Kisan Da Rundunar “SARS” Ta Nigeriya Ta Yi Wa Farar Hula A Jihar Delta

Al’ummar Nigeria suna ci gaba da nuna fushinsu akan yadda rundunar nan mai fada da manyan laifuka ta SARS ta yi wa wani farar hula a yankin Ugheli da ke jahar Delta.

ABNA24 : A jiya Lahadi ne dai kafafen sadarwa na al’umma su ka watsa bidiyon yadda rundunar ta SARS ta bude wuta aka wani matashi, sannan kuma su ka yi awon gaba da motarsa ta jeep, bayan da su ka bar gawarsa a kasa.

Mataimakin shugaban kasar ta Nigeria Yemi Osinbajo, da mataimakin shugaban Majalisar dattijai Ovie Omo-Agege da kuma karamin ministan aiki Festus Keyamo, suna cikin masu yin tir da halayyar ta rundunar SARS.

Mataimakin shugaban kasar ta Nigeria ya ce yanzu an wayi gari al’ummar Nigeria ba su iya tantance tsakanin ‘yan sanda da kuma ‘yan fashi.

Shi kuwa babban sufeton ‘yan sandan kasar ta Nigeria, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani aiki sintiri ko tsare hanyoyi da rundunar mai fada da fashi da makami take yi.

342/